Ana dakon sakamakon zaben Najeriya
February 27, 2023Hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ce tana sa ran karban sakamakon daga jihohi da dama a wannan rana ta Litinin kuma ta sha alwashin sanar da sakamakon da zarar ta kammala karbarsa.
A jiya Lahadi ne aka sa ran hukumar za ta sanar da sakamakon sai dai jihar Ekiti ce daya tilo da ta aike da sakamakon nata a shalkwatar tattara shi.
Jinkirin fidda wannan sakamakon dai ya fara saka shakku a zukatan al'ummar kasar, kasancewar ikirarin da hukumar ta INEC ta yi tun da farko na fitar da sakamakon ba tare da bata lokaci ba.
Wannan zaben da ya gudana a ranar Asabar din da ta gabata na zama mai zafi tun bayan da kasar ta koma kan tafarkin mulkin dimukradiyya.
A daya hannu a jihar Legas wasu bata gari sun afka wa hukumar zabe a yayin da ma'aikatanta ke tsaka da kidayar kuri'u.