1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yakin neman zaben Ghana ya yi zafi

Isaac Kaledzi Muntaqa Ahiwa/SB
October 28, 2024

Yakin neman zabe na can ya yi zafi a Ghana inda ake sa ran gudanar da babban zaben kasa da za a yi cikin makonni masu zuwa. ‘Yan Takara musamman na manyan jam'iyyun kasar dai na ci gaba da bayyana alkawuran sauye-sauyen.

https://p.dw.com/p/4mK4v
Ghana | Hagu zuwa dama: John Dramani Mahama da Mahamudu Bawumia masu neman shugabancin Ghana
Hagu zuwa dama: John Dramani Mahama da Mahamudu Bawumia masu neman shugabancin GhanaHoto: Nipah Dennis/AFP | OLYMPIA DE MAISMONT/AFP

Manyan ‘yan takarar neman shugabancin kasa a zaben da za a yi a Ghana cikin makon farko na watan Disamba, sun dukufa ne a yanzu wajen yin amfani da kalamai masu kama da fatawowi ga ‘yan kasar tare da alkawura. Mataimakin shugaban kasar mai ci, Mahamadu Bawumia, na jam'iyyar NPP na fuskantar hamayya mai zafi daga tsohon shugaban kasa John Dramni Mahama na jam'iyyar NDC, wanda ya mulki Ghana daga 2013 zuwa 2017.

Karin Bayani: Dambarwar siyasa a majalisar dokokin Ghana

Ghana | Masu zanga-zanga
Masu zanga-zanga a GhanaHoto: NIPAH DENNIS/AFP/Getty Images

Wannan ne karo na uku da John Mahama a Ghana ke neman takara, bayan shan kaye da ya yi a zaben 2016 da ma na 2020, inda Shugaba Nana Akuffo Addo na yanzu ya samu nasara. Manyan ‘yan siyasar da ke yakin neman zaben dai sun dauko salo na tallata manufofinsu daban-daban, sai dai kuma da dama daga cikin ‘yan Ghana na cewa babu wani sabon abu da suke ganin za a samar a kasar.

Mataimakin shugaban kasar mai ci, Mahamadu Bawumia na jam'iyyar NPP dai tsohon ma'aikacin babban bankin kasa ne, baya ga kwarewa a fannin tattalin arziki. Rungumar tsarin zamani na habaka tattalin arziki ta hanyar zamanin, alkawura ne da bangarorin biyu ke cewa za su kawo domin ciyar da Ghana gaba, amma duk da hakan gani kawai ‘yan Ghanar ke yi tamkar cika baki ne irin na ‘yan siyasa. Batu na tattalin arziki musamman koma bayansa, zai yi tasiri a zaben na Ghana, duk da cewa siyasar cikin jam'iyyu ma na iya sauya al'amura daga yadda ake ganin tafiyar al'amura a yanzun.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani