1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jam'iyyun NDC da NPP sun gwada kwanji a Ghana

October 14, 2024

Gangamin yakin neman zabe ya rikide ya koma tarzoma a tsakanin magoya bayan jam'iyyar adawa ta NDC da ta NPP mai mulki a kasar Ghana.

https://p.dw.com/p/4lme2
'Yan takarar jam'iyyar NDC John Dramani Mahama da na NPP Mahamudu Bawumia
'Yan takarar jam'iyyar NDC John Dramani Mahama da na NPP Mahamudu BawumiaHoto: Nipah Dennis/AFP/Getty Images, Olympia de Maismont/AFP

Ana zargin matasan bangaren jami'iyya mai mulki ta NPP da mallakar bindigogin da aka harba a yayin husumar da ta barke tare da jikkata mutane biyu. Fadan ya kuma haddasa fargaba kan makomar babban zaben kasar da ake shirin gudanarwa a karshen shekara ta 2024.

Karin bayani: Fargaba gabanin babban zabe a Ghana

Jam'iyyun NPP mai mulkin da NDC mai adawa na zargin juna da kokarin shafawa magoya bayansu kashin kaji, bayan barkewar rikicin. Masu sharhi na ganin cewa fannin siyasa a Ghana a yanzu ya zama tamkar wata dama ta zuba hannun jari, saboda haka ba mamaki idan masu 'yan siyasa da wadanda ke son fakewa da wannan suka fara amfani da fitina don mayar da kudadensu ta hanyar amfani da 'yan bangar siyasa.