1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martani kan dage lokacin zaben Najeriya

February 16, 2019

Kasa da 'yan sa'o'i da bayyana dage babban zaben Najeriya rudani da rashin tabbas na zaman makoma na manyan jam’iyyun kasar guda biyu na APC mai mulki da PDP mai adawa inda yanzu haka sun yi nisa a cikin zargin juna.

https://p.dw.com/p/3DV5b
Nigeria Wahl - Wahlkarten
Hoto: DW/K. Gänsler

Har ya zuwa ranar yau Asabar dai daga duk alamu manyan jam'iyyun Najeriya sun gaza girgijewa daga rudanin sauya lokacin zaben da ya buge su babu shiri cikin dare.

Tuni sun yi nisa a cikin zargin juna da ma nunin yatsa ga ita kanta hukumar zaben kasar INEC da suke fadin bata da gaskiya, kuma ba ta yi domin al'umma ta kasa.

Babu dai zato ba kuma tsamanni hukumar zaben ta ce akwai matsalar isar kayan aiki ya zuwa sassan kasar dabam-dabam, domin  haka ba ta da zabi face kara tsawon mako guda cikin burin komai zai dai dai.

To sai dai kuma  ga har a cikin jam'iyyu na kasar dai akwai banbancin ra'ayi game da matakin INEC, kama daga na shugabancin PDP da ke gani hukumar ta kasa kuma dole shugabanta ya sauka, ya zuwa hedikwatar kamfen din yakin neman zabe na dantakara na PDP da ke ganin daga zaben yai dai dai a bisa dalilan da a cewar Engineer Buba galadima da ke zaman kakakin yakin neman zaben.

Wanin hani ga Allah baiwa ne ko kuma kokari na biyan bukata ta wasu dai, da ranar yau ne aka tsara shugaban hukumar zaben na kasa Farfesa Mahmoud Yakubu zai gana da masu ruwa da tsaki da harkokin zaben da nufin cikakken bayanai na hujjar INEC din na dage zaben.

To sai dai kuma ga jam'iyyar APC mai mulki dage zaben ya tabbatar da hadin bakin da ke tsakanin masu adawa na kasar da jami'an hukumar a mataki na kasa.