Arangamar 'yan sanda da 'yan Shi'a a Sokoto
December 27, 2019Talla
Rikicin ya barke ne bayan kammala sallar Jumma'a inda 'yan Shi'ar suka fito yin tattaki domin nuna rashin jin dadinsu kan ci gaba da tsare jagoransu Malam Ibrahim El-zakzaky da mai dakinsa, inda suka bayyana cewa an kai masu hari da bindiga.
Magoya bayan kungiyar IMN dai sun zargi jami'an 'yan sanda da watsa masu barkonon tsohuwa kana daga bisani suka bude masu wuta da harsasai na gaskiya, Sai dai a hirarsu da wakilinmu na jihar ta Sokoto Ma'awuya Abubakar Sadik kakakin rundunar 'yan sandan jiha ASP Muhammad Sadiq Abubakar ya musanta labarin bude wutar.