Sabon harin 'yan bindiga a Katsina
July 6, 2021Wannan lamari dai ya mayar da hannun agogo baya a kokarin da ake na magance matsalolin tsaro a wannan yanki na karamar hukumar Batsari, tar da sanya al'ummar yankunan shiga firgici. A baya dai al'ummar na ganin sun fara samun saukin hare-haren 'yan bindigar, sai gashi kwatsam wannan aika-aika ta faru a kauyen na Tsauwa. Bayan halaka mutanen 19 dai, 'yan bindigar kuma sun kwashi kaya tare kuma da kone garin kurmus.
Karin Bayani: Rashin tsaro da makomar ilimi a Najeriya
DW ta yi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Katsina SP Gambo Isa dai, wanda ya nunar da cewa zai tuntubi DPO na 'yan sandan karamar hukumar ta Batsari, sai dai daga bisani ya ce ya neme shi amma bai same shi ba amma zai ci gaba da neman sa. Gwamnonin da jihohinsu ke fuskantar ta hare-hare da sace-sacen 'yan bindigar da ke zuwa kauyuka da makarantu, sun yi ta yekuwar cewar al'umma su fito su kare kansu. Kashe wadannan mutane na zuwane a daidai lokacin da damuna ta fara kankama kuma babu abin da al'ummar yankunan karkara suka dogara da shi sai noma.