1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Najeriya: INEC ta kara wa'adin karbar katin zabe

Uwais Abubakar Idris AH
February 8, 2019

A matakin da ke nuna kokari na biyan bukatar masu korafe-korafe na rashin karbar katin jefa kuri’a, hukumar zabe mai zaman kanta ta Najeriya INEC ta sanar da kara wa’adin karban katin zabe.

https://p.dw.com/p/3D1pn
Wannan wani tohon hoto ne masu karbar katin zabe da muka yi amfani da shi a zaben Najeriya na baya
Wannan wani tohon hoto ne muka yi amfani da shi a zaben Najeriya na bayaHoto: Reuters/Sotunde

Hukumar zaben Najeriyar ta ba da kai bori ya yau bayan matsin lamba daga jam'iyyun 'yan dawa da dama na Najeriyar musamman ma dai jam'iyyar PDP da suka bayyana bukatar a kara wa’adin lokacin karbar katin jefa kuri’ar na din-din-din watau PVC, wanda sai da shi ne duk wanda ya samu rijista zai iya jefa kuri’a a zaben da za’a yi a mako mai zuwa. Maimakon dakatar da wannan aiki a Juma’ar nan a yanzu hukumar zaben ta kara wa’adin zuwa ranar Litini 11 ga watan Febrairun nan, tare ma da karin wa’adin lokacin da jami’an hukumar za su rarraba wannan kati da zai hada da ranakun Asabar da Lahadi.