1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Asusun IMF ya sake bai wa Ghana rancen Dala miliyan 360

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
April 14, 2024

Ghana wadda ta yi fice wajen arzikin Cocoa da Gwal da kuma man fetur, za ta yi amfani da bashin na IMF wajen habaka tattalin arzkinta da kuma sake fasalta tsarin bashin da ake binta

https://p.dw.com/p/4ejdg
Hoto: Maksym Yemelyanov/Zoonar/picture alliance

Asusun bada lamuni na duniya IMF ya amince da sake bai wa Ghana rancen Dala miliyan 360, domin farfado da komadar tattalin arzikin kasar da ya shiga mawuyacin hali a baya bayan nan.

Karin bayani:IMF: Bashin dala biliyan uku ga Ghana

IMF din da Ghana sun amince da yarjejeniyar bayan nazarin da asusun ya yi kan bashin Dala biliyan 3 da ya alkawarta bai wa kasar a cikin watan Mayun bara, inda ya zuwa yanzu ta karbi Dala biliyan daya da rabi.

Karin bayani:Ghana ta samu racne dala bilyan uku

Tun a shekarar 2022 ne tattalin arzikin Ghana ya fuskanci tabarbarewa mafi muni a tarihi, inda hauhauwar farashin kayayyaki ya haura kashi 50 cikin 100.

Ghana wadda ta yi fice wajen arzikin Cocoa da Gwal da kuma man fetur, za ta yi amfani da bashin na IMF wajen habaka tattalin arzkinta da kuma sake fasalta tsarin bashin da ake binta.