ASUU: Yajin aiki babu gudu babu ja da baya
August 29, 2022Taron majalisar zartarwar ASUU a Abuja ya ce babu gudu babu ja da baya a yajin aikin da ya dauki watanni shida kuma ya kai ga gurgunta daukacin harkaokin ilimi a jami'o'in tarrayar Najeriyar.
ASUU dai ta ce ba za ta sake kallon hanyar azuzuwa ba har sai gwamnatin kasar ta biya daukacin bukatunta wadanda suka hada da aiwatar da yarjejeniyar da ta cimma da gwamnatin kasar a shekarar 2009. Bayan nan kungiyar na neman a yi amfani da manhajjar biyan albashin malaman jami'o'in da ASUU ta gabatar wa mahukuntan kasar.
Ci gaba da yajin aikin dai ya kai karshen fatan sake komawa aji a bangaren daliban da suka share watanni shida, kuma ke shirin asarar daukacin sherar karatu ta bana.
Janye yajin aikin a bangaren ragowar ma'aikatan jami'o'in kasar tun da farkon fari ya haifar da fata cewar malaman za su bi sahu wajen janye yajin aiki kafin sabon matakin da ke zaman gagarumin koma baya a matsalar da ke barazanar kai kasar ga asara mai girma a harkar ilimi.
Farfesa Nasir Fage na zaman tsohon shugaban kungiyar ASUU na kasa da kuma yace hakuri ya zama wajibi a banagren iyaye da dalibai a kokarin neman kai karshen matsalar ilimin da ke dada lalacewa cikin kasar a halin yanzu.
A yayin da ASUU ke fadin gyara dole yawan daliban da ke kammala karatu a bana sun zarta na kowane lokaci a shekaru 20 da suka gabata.
Ko ya zuwa watan yunin da ya wuce sama da dalibai 60, 000 kasar Birtaniya ta bai wa izinin karatu a kasar daga tarrayar Najeriya. Abun da ke nufin kashe miliyoyi daloli, a tarrayar Najeriyar da ke korafin matsin tattalin arziki a halin yanzu.
Sa'idu Sambo kaftan na sharhi kan harkar ilimi kuma ya ce matakin yajin aikin na dada mayar da jami'o'in kasar baya tare da gina jami'o'in wajen da ke murna da rikicin.
To sai dai koma yaya ta ke shirin kayawa a tsakanin malaman da ke fadin sai an gyara, da kuma iyaye da ke kukan rashi, sannu a hankali yajin aikin na ASUU na kara kusantar yakin neman zabe. Kuma daga dukkan alamu siyasar na shirin yin tasiri a bangaren gwamnatin da ke neman mulki da masu adawar da ke kokawar kwacewa.
A fadar Adamu Garba da ke zaman jigon jam'iyyar APC mai mulki, yan ASUU sun rikide ya zuwa jam'iyyar adawa da ke neman hanyar kai karshen mulkin APC maimakon gyaran harkar ilimi.