AU na fargabar barkewar annobar kyandar biri a Afirka
October 31, 2024Hukumar lafiya ta Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi gargadi a Alhamis din nan kan cewa har kawo wannan lokaci ba a shawo kan cutar kyandar biri da ake wa lakabi da Mpox ba, tare kuma da kiran kasashen kungiyar da su hada kai don guje wa barkewar gagarumar annoba da ta fi Covid-19 muni.
Kawo yanzu dai cutar ta Mpox ta yi ajalin fiye da mutane 1,000 a Afirka a cikin mutane kusan 48,000 da suka kamu da ita, kamar yadda alkaluman da cibiyar rigakafin cutuka masu yaduwa ta nahiyar suka nunar. Galibin mace-macen da cutar ta haddasa sun auku ne a Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango inda cutar ta fi kamari duk da matakin yin allurar rigakafi da mahukuntan kasar suka dauka a farkon wannan wata.
Karin bayani:Jamus na taimaka wa Kwango gano masu fama da kyandar biri
Kungiyar ta Tarayyar Afirka ta ce lamarin ya fara zama abin damuwa a kasar Yuganda inda aka ba da rohoton mutuwar mutum na farko da ya kamu da cutar ,yayin da adadin sabin kamuwa ya karu zuwa mutane 830.