Jamus na taimaka wa Kwango gano masu fama da kyandar biri
August 21, 2024Gwamnatin Jamus ta sanar da aika dakin gwaje-gwaje na tafi da gidanka zuwa Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango don taimaka gano wadanda ke dauke da cutar kyandar biri.Fadar mulki ta Berlin ta kuma bayyana shirin horas da kwararrun jami'an kiwon lafiya dabarun gane alamomi kamuwa da Mpox da kuma sanar da jama'a matakan rigakafi. Ministar raya kasashe Svenja Schulze ta ce kasashen Afirka ne nemon taimakon duniya don tikarar cutar kyandar biri, kuma ya wajaba a kan Jamus ta ba da wannan taimako.
Karin bayani: Kyandar biri: AU ta ce annobar na karuwa a Afrika
DR Kwango ce ke kan gaba a duniya wajen kamuwa da cutar Mpox da ma dai bullar wani sabon nau'i da ake kamuwa da shi cikin hanzari. Tuni dai Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana sabon nau'in kyandar birin a matsayin abin damuwa kuma ta yi gargadin cewa yana iya yaduwa zuwa wasu kasashe. Cutar Mpox ba ta da saurin yaduwa kamar COVID19 kuma WHO ta ce ba ta tsammanin cewar za ta iya salwaantar da rayuwa ko dagula zamantakewar al'umma kamar yadda cutar sarkewar nunfashi ta yi.