AU ta nemi Senegal da ta gaggauta shirya zaben shugaban kasa
February 5, 2024Kungiyar hadin kan kasashen Afirka AU ta nemi kasar Senegal da ta gaggauta gudanar da babban zaben shugaban kasar, bayan da shugaba Macky Sall ya dakatar da zaben da aka shirya gudanarwa a ranar 25 ga wannan wata na Fabarairu.
karin bayani:'Yan adawa sun yi watsi da dage zaben Senegal
Wannan na cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar Mousa Faki Mahamat ya fitar a Lahadin nan, kamar yadda kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ya rawaito, yana mai bukatar ganin an gudanar da zaben cikin gaskiya da adalci.
Karin bayani:Kotun Kolin Senegal ta jaddada hukuncin dauri kan madugun adawa Ousmane Sonko
A Litinin din nan ce 'yan majalisar dokokin Senegal za su yi muhawara kan ko za a iya gudanar da zaben a ranar 25 ga watan Agusta mai zuwa. zanga-zanga da kuma arangama da jami'an tsaro a kasar ta barke bayan da shugaba Macky Sall ya sanar da dage zaben sakamakon cukumurdar da ta dabaibaye tsarin fitar da 'yan takara.