'Yan adawa sun yi watsi da dage zaben Senegal
February 4, 2024Shugabannin jam'iyyun adawa da dama a Senegalsun ce za su kaddamar da yankin neman zabe kamar yadda aka tsara a can baya, kana kuma za su ci gaba da bijerewa matakin da shugaba mai barin gado Macky Sall ya dauka a ranar Asabar wanda ke karo na farko tun bayan shekarar 1963.
Karin bayani: Senegal: Shugaba Sall ya dage zabe
Daga cikin wadanda suka yi fatali da matakin dage zaben har da fitaccen dan adawa Khalifa Sall, da kuma tsohuwar firaminstar kasar Aminata Touré. Dukanninsu sun isar da kiraye-kiraye na a fito zanga-zanga a ranar Lahadi (04.02.2024) domin ceto kasar daga ta'addancin dimukuradiyya.
Tun dai bayan sanar da dage zaben har sai baba ta gani, kungiyar habaka tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika ECOWAS da ma'aikatar harkokin wajen Amurka suka bayyana damuwa tare da kira da a gaggauta sake tsayar da sabuwar rana da sharuddan gudanar da zabe sahihi cikin 'yanci da adalci.