1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

AU ta taya Tinubu murnar lashe zabe

March 4, 2023

Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka AU, ya taya murna ga zababben shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu na lashe babban zaben kasar da ya gabata.

https://p.dw.com/p/4OFTE
Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, Mahamat Moussa Faki
Shugaban kungiyar Tarayyar Afirka, Mahamat Moussa FakiHoto: John Thys/AFP

A cikin sanarwar da Moussa Faki Mahamat ya fitar, ya ce za a amshi dukkanin korafe-korafe kan zaben bisa dokokin Najeriyar yayin da jam'iyyun adawa ke zargin an tafka magudi a babban zaben kasar. Ya kuma mika bukata ga dukkanin jam'iyyun adawar da su wanzar da zaman lafiya tare da bin dokokin kasar.

Kimanin mutane miliyan 25 ne suka kada kuru'u a ranar Asabar din data gabata a Najeriyar, wanda ya bai wa shugaban mai jiran gado Bola Ahmed Tinubu nasarar lashe zaben da kuru'u kimanin milyan 8 da dubu dari 8.