Matsalar wutar lantarki a Najeriya
September 14, 2023Talla
Lantarkin da ake samu ta National Grid ya dauke gabaki daya a safiyar wannan rana, sai dai an ce sannu a hankali yana dawowa amma dai har yanzu bai kai ga adadin da al'umma ke sha a kowace rana ba.
Najeriya da ke da yawan al'umma a nahiyar Afirka na samar da megawats sama da dubu 12 amma kuma ko kashi daya cikin kaso hudu na adadin al'ummar kasar basa samu.
Babbar tashar da ke rarraba lantarki ga 'yan Najeriya ta samu matsala sama da sau biyar a shekarar 2022.
A baya an kashe biliyoyin kudi a kokari na magance matsalar wutar lantarki da kasar ke fama da shi amma abin ya ci tura. Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sha alwashin kawo karshen matsalar wutar lantarki da ta zame wa kasar karfen kafa.