1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Babban taron jam'iyyar PDP ya gagara

Muhammad Bello/ MNAAugust 17, 2016

Jami'an tsaro a Fatakwal sun hana kowa shiga zauren babban taro a sakamakon wani hukuncin kotu cewar taron haramtacce ne.

https://p.dw.com/p/1Jjso
Nigeria Regierungspartei PDP
Hoto: DW/K. Gänsler

Babban taron jam'iyyar adawa ta PDP a Najeriya da ke da nufin zaben sabbin shugabanninta ya gagara. Hakan dai ya zo ne bayan kammala dukkanin shirye-shirye don gudanar da taron a wannan Laraba, amma jami'an tsaro da aka jijjibge sun hana kowa shiga harabar da aka shirya yin wannan taro a sakamakon wani hukuncin na kotu cewar taron na jam'iyyar ta PDP haramtacce ne.

'Yan PDP dai da suka barko daga sassa dabam-dabam na Najeriya don halartar wannan taro sun kwana a birnin Fatakwal tare da wayar gari cike da fatan taron zai gudana, amma kwatsam sai ga tarin jami'an tsaro dauke da bindigogi an girke su a ciki da kewayen inda za a yi wannan taro, wanda kuma hakan ke nufi taron bai yiwu ba a wannan Laraba.

Hukuncin babbar kotun Abuja ya yi aiki

Bayanan da jami'an tsaron ke da shi dai shi ne cewar babu wani hukuncin kotu kan wannan taro da ya dara na babbar kotu da ke Abuja da ta ce kada jam'iyyar ta PDP ta sake ta gudanar da wannan taro a sakamakon karar da Sanata Ali Modu Shariff da ke ikirarin cewar har yanzu shi ne shugaban jam'iyyar ya kai gabanta.

Cin alwashin da jam'iyyar dai ta PDP ta yi kan wannan taron nata ba karami ba ne. Amma da farko an jiyo Gwamna Wike na jihar Rivers da ke zaman jagoran kwamitin tsara taron da ya gagara na bayanin cewar sun shirya tsaf.

Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf
Shalkwatar jam'iyyar PDP a birnin AbujaHoto: DW/U.Haussa

Kan babban taron na PDP da ya gagara a karo na biyu cikin watanni hudu, Barister Abdullahi Jalo tsohon mataimakin kakakin jam'iyyar ta PDP na kasa mai kuma san tsayawa matsayin mataimakin shugaban jam'iyyar ta PDP cewa ya yi.

"Bai kamata a bari ma'aikatar shari'a tana irin wannan cin fuska ba. Ya kai sati biyu kotu a fatakwal ta ce kada wata kotu ta hana mu wannan taro. Kuma kada hukumar zabe ta yi wani saibi na rashin zuwa, ta zo ta zama mai yanke hukunci na ganin an yi adalci a wannan taro na PDP."

Shi kuwa tshohon gwamnan jiahar Sakkwato da kuma ke cikin kwamitin tsare-tsaren taron na PDP Alhaji Dalhatu Bafarawa kokawa ya yi kan adawa a kasar yana mai kira ga gwamnati da ta ba wa 'yan hamaiya dama su yi abubuwan da suka sa a gaba matukar yana kan doka.

Makarfi zai ci gaba a matsayin shugaban riko

Wata shugabar mata 'yan PDP a jihar Sakkwato da ita ma ta je birnin Fatakwal don wannan taro da yaki yiwuwa, Hajiya Rabi Amadu Giyawa cewa ta yi.

"Duk manyan jam'iyyar PDP sun hallara sun kuma shirya gudanar da wannan babban taro, amma wannan mutumin da nake gani ba dan jam'iyyar PDP ba ne yana son ya wargaza jam'iyyar. Bukatarsa ba za ta boya ba."

Yanzu dai kwarya-kwaryar taron kusoshin jam'iyyar ta PDP a cikin gidan gwamnatin jihar Rivers ya amince da karawa mai rikon jam'iyyar a yanzu wato Sanata Ahmad Makarfi, karin wa'adin shekara guda kan kujerar shugabancin jam'iyyar kafin jam'iyyar ta kai ga iya daidaita kanta don sake tsara wani babban taron da zai kai ga gudanar da zabubbukan cikin gida na PDP da har yanzu ya gagara.