Badakalar safarar kananan yara a kasar Nijar
June 23, 2014Jaridar "L'evenement" da ke zaman kanta ce ta fara bankado wannan labarin fataucin yara kanana tun farkon wannan shekara ta 2014. Ta nunar da cewar akwai hannu wasu manyan jami'an gwamnatin Nijar da suka mallaki irin jarirran da aka yi safararsu daga kudancin Najeriya. Saboda haka ne hukumomin shari'a suka rungumi wannan batu tare da gudanar da bincike bisa hadin guywar hukumomin 'yan sanda na Nijeriya da Nijar da Benin da kuma Burkina Faso. Lamarin da ya basu damar sauraran duk mutanen da ake zargi da hannunsu a ciki safarar yara kananan.
Adadin wadanda aka kama
Kimanin mutane 20 suke hannun 'yan sanda a halin yanzu, ciki har da wadanda ake zargi da mallakar 'ya'yan na jabu da jami'an gidajen asibiti da na ma'aikatun magajin gari da ake zargin an hada baki da su domin yin takardun
haihuwar jarirrai na boge. Daga cikin wadanda suka je ofisin 'yan sanda don yi musu bayani, har da mai dakin shugaban majalisar dokokin Nijar Hama Amadou.
Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka soma tofa albarkacin bakinsu a kan wannan batu. Moustafa Kadi na kungiyar CODAE ya bayyana gamsuwarsa game da matakin da hukumomin suka dauka. Amma kuma ya ce ya na fatan za a yi adalici a cikin lamarin na safarar yara kanana. Hukumar 'yan sandan Nijar da ma'aikatar shari'a ta kasar ba su yi bayani a kan wannan batu ba, da kuma takamaiman zargin da ake yi wa wadannan ake ci gaba da sauraransu a cibiyar 'yan sandar ba.
Mawallafi: Gazali Abdou
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe