Badakalar satar kudi a kamfanin NNPC
March 23, 2016Talla
A Najeriya an tuhumi kamfanin man fetur mallakar gwamnatin kasar da boye biliyoyin kudi, a daidai lokacin da gwamnatin shugaba Buhari ta matsa kaimi don sanin irin badakalar mai da aka yi, gabanin ya karbi mulkin kasar. Tuni kuma shugaban na Najeriya ya dukafa wajen sake fasalin bangaren mai na kasar. Wata kungiya mai zaman kanta ta ruwaito cewa, ta gano a zamanin mulkin tsohon shugaba kasa Goodluck Jonathan, an yi sama da fadi na Euro biliyan 22 a tsakanin shekara ta 2011 izuwa 2015. Kamfanin man na NNPC, ya musanta batar da kudin da ake fada, inda NNPC yake cewa wai masu zargin basu yi bincike na hakika ba.