Shirin ilmantar da fursunonin Najeriya
December 28, 2021Cikin wadanda za su ci gajiyar shirin, har da fursunonin biyar da ke karatun digiri na uku watau Phd, wanda sauyi ne daga tsarin da ake da shi a baya a kasar. Wadannan fursunonin da suka aikata laifuffuka iri dabam-dabam ake tsare da su a gidan kaso, amma a wannan yanayi 72 daga cikinsu suka samu damar fara karatun digiri, biyar ke karatun digiri na uku da suka amsa ranstuwar fara karatu.
Wata dabara ce da hukumar kula da sauya halayen fursunonin da jami’ar karatu daga gida watau NOUN suka tsara, don sauya halayen fursunonin su zama mutanen kirki, ta yadda za su zamo masu amfani da kansu da ma Najeriyar.
Fursunonin 72 da yanzu suke karatun digiri dukkaninsu daga gidan yarin Kuje da ke Abuja suke karatun. Tun bayan da aka sauyawa hukumar kula da gidajen yari ta Najeriya suna zuwa hukumar gyara halaye, aka tsara hanyoyin da za’a sauya tunani da halayen na fursunonin ta yadda za su zama mutanen kirki ko bayan sun kamalla zaman gidan yari a kasar.