Bam ya halaka mutane 20 a Zariya
July 7, 2015Wani bam da ya tashi a birnin Zazzau da ke arewacin jihar Kaduna a Najeriya ya yi sanadin kisan mutane ashirin da biyar yayin da wasu 35 suka jikkata.
Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa'i ya bayyana haka a shafinsa na Twitter inda ya ce ya kadu da jin wannan mummunan labari.
Zinari Shehu wata 'yar Jarida a garin na Zariya ta bayyana cewa bam din ya tashi ne da misalin karfe goma agogon na Najeriya wato tara kenan agogon GMT da Ghana a sakatarriyar Gogarawa karamar hukumar Sabon Gari.
Wasu da suka sheda lamarin sun bayyana cewa mafi yawa wadanda suka rasu sun kasance mata da suka je aikin tantance ma'aikata da ke wakana a jihar ta Kaduna.
Cikin wadanda wannan hari ya ritsa da su har da karamin yaro dan shekaru biyu a cewar wadanda lamarin ya faru a gabansu.