Zanga-zangar adawa da gwamnati a Bangladesh
August 2, 2024Talla
Masu boren dai na neman firanminista Bangladesh, Hasina ta sauka daga mukaminta tare da neman 'yanci ga iyalan mutum 150 da aka kashe lokacin zanga-zanga dalibai kan tsarin daukan aiki a kasar. An ruwaito cewa, jami'an 'yansanda sun tarwatsa masu zanga-zangar da hayaki mai sa hawaye da kuma harsashen roba a arewa maso gabashin garin Habibganj.
Karin bayani: Daliban Bangladesh sun sha alwashin ci gaba da zanga-zanga
Rikicin da kasar ta fada a wannan lokacin shi ne bore mafi girma da gwamnatin Hasina ke fuskanta, bayan wata zanga-zangar da aka yi a lokacin da ta yi tazarce a karo na hudu a kan karagar mulkin kasar, sakamakon lashe zaben watan Janairun 2024 da 'yan adawa suka kauracewa.