Najeriya: Rikicin shugabanci a Jam'iyyar adawa ta PDP
March 23, 2022Babbar Jamiyyar adawa ta PDP a Najeriya na ci gaba da samun rarrabuwar kawuna na bangaranci tsakanin kudanci da Arewacin kasar kan batun dan takarar shugabancin kasa inda yanzu shiyyar kudu maso kudancin Najeriya wato Niger Delta ke barazanar cewar muddin jamiyyar ba ta ba yankin damar tsayar da dan takarar ba to kuwa za ta balle daga jamiyyar. Hakan kuwa na zuwa ne yayin da sauran sassan kasar musamman yankin Igbo ke matsa lambar su ma a basu wannan takarar.
Gaggan 'yan jamiyyar ta PDP a yankin na Niger Delta da ya kunshi jahohin Bayelsa da Rivers da Akwa Ibom da Delta da Edo da kuma Cross Rive sun yi taro a jihar Akwa Ibom inda suka fidda matsayar su cewar muddin yankin na su bai samu tikitin takarar shugaban kasa ba to kuwa za su balle daga jamiyyar.
Taron dai da ya samu halartar wasu daga gwamnonin yankin su shidda, da tsoffin gwamnoni da 'yan Majalisun tarayya da sauran ma su fada aji na yankin. Taron dai ya yi la'akari ne da yadda jamiyyar ta PDP ta ringa samun tagomashin zabe a yankin tun bayan dawowar mulkin dimukuradiyya a kasar a shekarar 1999.
Sai dai yayin da yankin na kudu maso kudancin Najeriyar ke matsin lambar a basu takarar shugabancin kasa ko kuma ta watse tuni sauran yankunan kasaar ke nuna irin wannan muradi musamman yankin kudu maso gabashin kasar na kabilar Igbo.
Farfesa Usman Kibon babban malami a daya daga manyan jami'oin kasar kuma mai sharhi kan alammuran siyasa yace ya kamata a yi hattara.