1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Barazanar tashin hankali a zaben Najeriya 2023

Uwais Abubakar Idris ZMA
January 18, 2023

‘Yan siyasa da masharhanta na maida martani a kan gargadin da kungiyar ECOWAS da Majalisar Dinkin duniya suka yi ga Najeriya a kan rigigimun siyasa gabanin gudanar da zaben kasar.

https://p.dw.com/p/4MNss
Nigeria Wahlen l Wähler gibt Stimme ab, Lagos
Hoto: Stefan Heunis/AFP

Daga kalamai na habaici da tsokana zuwa ga masu zafi na zargin juna da ma takala da ka iya zama fitina ne ke fitowa daga bakin ‘yan takarar neman shugabancin Najeriyar musamman na jamiyyun APC mai mulki, da na ‘yan adawa ta PDP ta Labour da NNPP a dai dai lokacin da yakin neman zaben ke kara zafi a cikin kasar.

Wannan na faruwa a lolacin da Majalisar Dinkin Duniyar da kungiyar raya tattalin arzikin yankin Afrika ta yamma suka yi wannan gargadi na Najeriyar ta yi hankali da shiga rigingimu na siyasa.

Zabe a Najeriya dai babban al'amari ne domin kuwa yawan masu jefa kuri'a ya nuna tamkara zabe ne a kasashen yankin Afrika ta yamma 15. Ana dai nuna ‘yar yatsa ne a kan a wannan harka musamman matasa da ake amfani da su wajen tada hargisti, inda tuni kasar ta fara ganin hakan. 

Ci gaba da fuskantar kai hare-hare a kan ofisoshin hukumar zaben Najeriyar da ma kan jama'a a wasu sassan Najeriya na tada hankali sosai ga zaben kasar. To sai dai shugaban hukumar zaben Najeriya ya jaddada cewa wannan ba zai hana gudanar da zaben ba.

Kungiyar ECOWAS da MDD dai na fatan Najeriyar za ta tabbatar da an gudanar da zabe cikin kwanciyar hankali, fatan da ke zukatan mafi yawan ‘yan kasar da ke kaunar zaman lafiya da ci gaban ta.