Salon rayuwaGhana
Ghana: Barazanar tsadar rayuwa
May 16, 2024Talla
Wannan tsadar rayuwa dai ta sanya a yanzu haka kowane magidanci ke bukatar kimanin Cedi 600 a mako guda kwatankwacin dalar Amurka 45 domin yin cefane, cikin albashin da bai wuce Cedi 3000 kwatankwacin dalar Amurka 200 ba. Tsadar kayan abinci a yanzu ta kai dukunun Cedi daya ya koma biyar, inda a wasu wuraren ma barkonon da ake hadawa da shi sayar shi ake. Koko da kosai ya tashi daga Cedi hudu zuwa 10 hakan nan tumatiri kwalli daya tak madaidaici kusan Cedi biyar ke nan, al'amarin da al'umma ke cewa tsananin ya fara kamari. Wannan matsala dai na haifar da fargabar samun barazanar karancin abinci a Ghana, idan masu ruwa da tsaki ba su yi wa tufkar hanci ba.