Zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a Ghana
November 11, 2022Koda yake matsalar sauyin yanayi ma na yin mummunan tasiri ga al'ummar kasar ta Ghana, batun tsadar rayuwa ne ya sanya aka fara zanga-zangar adawa da shugabancin Nana Akufo-Addo. Duk da cewa ya yi kiran a kwantar da hankula a gidan talabijin din kasar, hakan bai sa masu nuna fushinsu kan halin da kasar ke ciki sun ja da baya daga nuna gazawarsa ba.
Karin Bayani: Tashin farashi ya addabi Ghana
Bacin ran daruruwan masu zanga-zangar adawa da shugaban kasar mai ra'ayin 'yan mazaan jiya Nana Akufo-Addo ta ruru ne, sakamakon tsadar rayuwa da al'ummar Ghana ta tsinci kanta a ciki. Tsadar kayayyaki da ta mamaye duniya, na shafar kasar sosai. Arne Wulff da ke zaman shugaban gidauniyar Konrad-Adenauer ta Jamus a kasar ta Ghana, ya yi karin haske kan yadda faduwar darajar kudin kasar wato Cedi ke matukar shafar rayuwar al'umma yana mai cewa:
"A watan Oktobar da ya gabata, darajar kudin kasar wato Cedi ta sauka a kan dalar Amirka da kaso sama da tara. Cikin kusan makonni hudu, yanzu ana canza kowacce dalar Amirka guda a kan Cedi dubu 13 da 875. Haka ma ake sauya kudin euro, Darajar kudin Ghana ta sauka sosai, a daidai lokacin da farashin kayayyaki ya yi tashin gauron zabi. Hakan ya sanya rayuwar al'ummar kasar cikin kunci, kuma babu makawa wannan na daga cikin dalilin zanga-zangar.''
Sai dai matsalolin sun wuce haka. Masu zanga-zangar na dauke da kwalaye da aka yi rubutu kamar haka: "Talauci na karuwa" da "muna bukatar sabon kundin tsarin mulki" da kuma "Ghana ce kawai kasar da ake aikata muggan laifuka".
A ranar Talatar da ta gaabata gabanin tashinsa zuwa taron sauyin yanayi na duniya da ke gudana a yanzu haka a kasar Masar wato COP27, Shugaba Nana Akufo-Addo ya yi alkawarin tabbatar da ganin an samar da kudin tallafi kan dumamar yanayi da aka jima ana ce-ce-ku-ce a kansa, sai dai duk da haka ana ganin wannan ba zai magance matsalar tsadar rayuwa da al'ummar Ghana ke ciki ba.