INEC ta tabbatar da nasarar PDP a Bayelsa
February 14, 2020Babu dai zato ba kuma tsammani kotun kolin tarrayar Najeriyar ta kai ga soke shirin jam'iyyar APC da ta yi nasarar kwace goruba a hannun kuturu a zaben gwamnan jihar. Bayelsan dai na zaman ta uku a cikin jeri na jihohin da suka kai ga fuskantar matsala a bangaren jam'iyyar APC mai mulki da tun da farkon fari ta kai ga asara ta Zamfara ko bayan kasa shiga zaben gwamnan Rivers.Tuni dai nasarar 'yan Leman a cikin zauren kotun ta fara dauke hankali na 'yan kasar da ke kallon darusa dabam-dabam ga masu sana'a ta siyasar tarrayar Najeriyar dama 'yan kallo. Adamu Fanda dai na zaman ma'ajin jam'iyyar APC na kasar daya kuma a cikin masu zama na makoki na asarar mai zafi ga masu tsintsiyar 'yar mulki wanda ya ce rishin samun nasarar ta APC a Bayelsa babbar asara ce. Rikicin cikin gida dama kokari na dauki ka dora ne dai ya kai masu tsintsiyar ga asarar a Beyelsan, to sai dai kuma a fadar Lawal Nalado da ke zaman shugaban jam'iyyar Accord da ke kasar akwai babban darasi a cikin hukuncin da ya manta da bukatun al'ummar da ke bukatar sauyin na Bayelsa. Abun jira a gani dai na zaman tasirin masu takama da siyasar dama su kansu alkalai na kasar a kokari na karin karfi a cikin tsarin zaben Najeriya da ke da bukatar girma.