Bazoum ya nemi taimakon Amurka
August 4, 2023A cikin wata wasika da jaridar Amurka Washington Post ta wallafa, Mohamed Bazoum ya bayyana girman barazanar tsaron da ke tunkarar Nijar da ma yankin Sahel muddin aka amince da juyin mulkin da sojoji suka yi masa a ranar 26 ga watan Yuli.
Sai dai tuni sabuwar majalisar sojojin da ta karbe ikon kasar ta yi kashedi tare da shan alwashin mayar da martani mai zafi ga duk kasar da ta yi kasadar afka wa Nijar da karfin tuwo.
Furicin majalisar ta CNSP karkashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani na zuwa ne a daidai lokacin da wa'adin da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta ba wa sojojin domin mayar da shugaba Bazoum kan kujerarsa ke karatowa.
Sai dai a kokarin da ake na shawo kan lamarin cikin ruwan sanyi wata tawagar wakilai daga makwabciya Najeriya karkashin tsohon shugaban kasar janar Abdousalami Abubakar ta gana da bangarori daban-daban na Nijar a birnin Yamai to amma har yanzu Abuja ba ta sanar da matsayar da aka cimma da sojojin ba.