1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar ta yi muhawarar dakile ta'addanci

July 1, 2022

Kabilun Abzinawa da Larabawa da Toubawa da Fulani na jihar Agadez a yayin wani taro sun nuna wa shugaban Nijar manyan matakan da zai dauka idan har yana son dakile tashin hankali na 'yan tawaye da ya kunno kai a jihar.

https://p.dw.com/p/4DY9V
Deutschland Berlin | Treffen Angela Merkel und Mohamed Bazou aus Niger
Hoto: Presse- und Kommunikationsdienst der Präsidentschaft von Niger

Shugaba Mohamed Bazoum na Nijar ne dai ya jagoranci taron na kwanaki biyu. Kawo yammacin Jumma'a, lokacin da aka kammala taron, Shugaba Bazoum ya tattara matsalolin da mahalarta taron suka bayyana domin ganin an samu zaman lumana mai dorewa a yankin na Agadez. 

Jihar Agadez ce dai jiha mafi girma a Nijar, inda mutane sama da 400,000 ke zaune a wannan yanki mai iyaka da kasashen Aljeriya da Libiya da kuma Chadi. A matsayinta na wacce a shekarun baya ta yi fama da matsalar 'yan tawaye, har yanzu burbushinsu na neman kara habaka tashin hankali a yankin.

A yayin da yake jawabi Shugaba Bazoum ya ce ''za mu  karfafa duk wasu matakai na bin diddigin samun bayanan sirri domin yaki da annobar rashin tsaro''. Sai dai shugaban ya bukaci mutanen Agadez da su saki jiki, su rika bayar da bayanan sirrin ga hukumomi. 

Sojin Nijar a wani yanki na Agadez
Hoto: AFP/S. Ag Anar

''Muna jira mu ga irin gudunmawar da ku al'umma za ku bayar wurin magance fashi da makami da safarar miyagun kwayoyi.'' in ji Shugaba Bazoum

Mutanen da suka halarci taron daga arewacin jihar Agadez sun ji dadin yadda shugaban kasar ya halarci taron sannan kuma sun bukaci ya kara azama wurin ganin gwamnati ta dakile sabuwar matsalar tsaron da ke fuskantar yankin.

Sojin Nijar a fagen daga
Hoto: picture-alliance/Zuma/Planet Pix/A.F. Echols


Jagororin al'umma irinsu Idrissa Hamidan sun yi fatan taron habbaka zaman lafiyar zai taimaka wurin kawo karshen matsalolin yankin Agadez da ma Nijar gaba daya. ''Mun rubuta matsalolin da ke Agadez, mun mika wa shugaban kasa. Muna son ya dauki matakin da zai iya dauka domin kawo karshen matsalolin.'' in ji Hamidan