1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar kara bai wa mata dama a siyasa

Uwais Abubakar Idris LMJ
March 8, 2022

Dubban mata da masu fafutuka sun gudanar da wata gagarumar zanga-zangar lumana a Abuja fadar gwamnatin Najeriya, tare da yin koke kan nuna musu bambanci da wariya a harkokin siyasa.

https://p.dw.com/p/48Bl4
Zanga-zangar mata kan fyade a Abuja Najeriya
Fyade na daga cikin abin da ke ciwa mata tuwo a kwarya a NajeriyaHoto: DW/U. A. Idris

Mata dai sun yi wannan zanga-zanga ne, a daidai lokacin da ake bikin ranar mata ta duniya da aka saba gudanarwa a duk ranakun takwas ga watan Maris na kowacce shekara da nufin yakar cin zarafi da take hakkin mata a duniya. Masu zanga-zangar dai na son a kawar da nuna wariya da matan ke fuskanta a kuma ba su karin damarmaki na damawa da su a harkokin siyasar kasar, ta hanyar yin dokar da za ta tilasta hakan. Watsi da wannan yunkuri da 'yan majalisun dokokin Najeriyar suka yi, ya kara harzuka matan. Ladia Bala ita ce shugabar kungiyar mata 'yan jaridu ta Najeriya da suka jagoranci zanga-zangar:"Mun fito ne mu nuna rashin gamsuwa a kan abin da ya faru, sannan mu yi kira ga majalisa cewa wadannan dokoki da suka yi watsi da su, su dawo su sake gyara."

Najeriya Maiduguri | 'Yan Gudun Hijira I  Boko-Haram
A lokutan rikici dai, mata sun fi shiga cikin halin taskuHoto: Kristin Palitza/dpa/picture alliance

Wannan gangami dai ya samu karbuwa sosai, domin dukkanin fitattaun da ake ji da su a fafutukar kare hakokin mata sun hallara musamman ma dai mazan da suke fada aji kamar Farfesa Jibo Ibrahim manarzci a cibiyar dimukuradiyya da ci-gaban kasa CDD, kuma a cewarsa duk wani dan Najeriya ko 'yar Najeriya na da 'yanci, 'yancin nan kuma ba na maza ba ne ba na mata ba ne na kowa da kowa ne. Ya kara da cewa watsi da 'yan majalisar dokoki suka yi da wadannan kudurori, dole ne ya yi wa kowane dan Najeriya ciwo. Kwamared Hauwa Yusuf Gwaram ta ce tura fa ta kai bango, a dangane da haka suke neman gwamnati ta sa hannu a kan abin da mata ke bukata. A cewarta mata su suka fi yawa a Najeriya, kowane mataki ya kamata a ce mace tana samun kanta a ciki kila matan za su fi samun sauki a kan halin da mazan ke nuna musu. Bayanai dai na nuna cewa majalisar wakilan Najeriya ta sauya matsayin da ta dauka a kan kudurorin da suka shafi matan da aka yi watsi da su, abin da ke nuna ribar matsin lamba da jajircewar da suka yi.