1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bincike a kan jirgin da aka kama a Kano

December 7, 2014

Kasar Rasha ta bayyana cewa bata da masaniya dangane da jirgin daukar kaya na kasar da jami'an tsaron Najeriya suka cafke a Kano.

https://p.dw.com/p/1E0Vu
Hoto: picture-alliance/AP Photo

Ofishin jakadancin kasar ta Rasha a Najeriya ne ya sanar da hakan, inda ya ce ba shi da masaniya dangane da jirgin jigialr kayan da jami'an tsaro suka ce sun cafke a filin sauka da tashin jiragen sama na Malam Aminu Kano da ke Kanon a yankin arewa maso yammacin tarayyar Najeriya a wannan Asabar din.

Jirgin wanda rahotanni suka bayyana cewa ya taso ne daga Bangui babban birnin kasar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya a kan hanyarsa da zuwa N'Djamena na kasar Chadi ya yi saukar gaggawa ne a filin saukar jiragen saman na Malam Aminu Kano.

Wani daga cikin ma'aikatan filin saukar jirtagen saman na Malam Aminu Kano da ya nemi a sakaya sunansa, ya shaidawa manema labarai cewa a yanzu haka suna tsare da matuka jirgin da ma ma'aikatansa biyar 'yan asalin kasar Ukraine.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake fama da takaddama dangane da siyo makamai domin yakar kungiyar Boko Hara inda a watan Oktoban da ya gabata ma dai sai da hukumomin Afirka ta kudu suka cafke wani jirgin Najeriya makare da kudade kimanin dalar Amirka miliyan 15 da mahukuntan Najeriyar suka ce wai za su sayo makaman yakar Boko Haram ne da su.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Pinado Abdu Waba