Zargin binne masu zanga-zanga a boye
July 25, 2023Kungiyar mai kare hakin jama'a ta Amnesty International tace dole ne gwamnatin jihar Lagos ta dakatar da shirinta na bizne gawarwakin mutanen su 103 har sai an gudanar da cikakken bincike na dalilin mutuwarsu da ka ko su wanene, domin haka kawai bisa doka ba'a bada izini na bizne wanda ya mutu ba, musamman na mutane masu yawa. Wata takarda aka bankado ne ta tono al'amarin da aka so a yi a boye.
Karin Bayani: Najeriya na biyan diyyar asarar EndSars
Wadanda suka yi wannan zanga-zanga a wancan lokaci dai sun dage kan cewa lallai a idannunsu an kashe jama'a musamman ma dai a lokacin da jami'an sojoji suka afkawa masu zanga zangara a mashigar unguwar Lekki da ke Lagos. Deji Adeyanju daya ne daga cikin shugabanin da suka gudanar da zanga zangara awancan lokaci.
Bankdo wannan shiri na bizne mutanen 103 da har gwamnatin ta samar da kudi sama da Naira milyan 61, ya sanya gwamnatin jihar Lagos amsa cewa lallai akwai shiri na biznen mutanen amma ba wadanda suka mutu bane a lokacin zanga-zangar Endsars. A sanarwar ta gwamnatin ta fitar tace a tuna an samu arcewa fursunoni a gidan yarin jihar inda aka kashe mutane da ma a wasu rigingimu. A wancan lokaci dai gwamnan jihar ta Lagos Sanwo Olu ya bayyana cewa.
Da alamun bayanai da ma dalilai na kare kai basu gamsar da mutanen da dama ba, ko me kungiyar ta Amnesty International ke son ganin an yi a yanzu? Ta dai bukaci ganin an yi bincike na hakika. A yayin da ‘yan Najeriya suka sa ido don ganin gaskiyar lamarin masu sharhi na bayyana cewa gaskiya ce za ta yi halinta domiin kuwa ita karya hure take ba ta ‘ya'ya.