Ambaliyar ruwa ta mamaye Maiduguri
September 13, 2024Masu aikin ceto na ci gaba da zakulo gawarwaki da kuma mutane da suka makale a birnin Maiduguri na jihar Borno sakamakon mummunar ambaliyar da ta afka wa garin. Ya zuwa yanzu hukumar agajin gaggawa ta kasar NEMA ta ce mutum kusan arba'in ne aka tabbatar da mutuwarsu kuma ana ci gaba da aikin ceto.
Karin Bayani: Aikin ceto na tafiyar hawainiya a Maiduguri bayan ambaliya
Gwanayen ninkaya da kuma sauran ma'aikatan agaji ke aikin ceto mutane da suka makale walau a kan rufin gidaje ko kuma kan bishiyoyi da ma sauran wurare a Maiduguri ke nan. Hukumar agajin gaggawa ta Najeriya NEMA ta ce mutane kusan arba'in ne ambaliyar ta yi sanadiyyar mutuwarsu baya ga sama da miliyan daya da ta raba da muhallai. Itama hukumar ba da agajin gaggawa ta jihar Borno ta bakin babban darektanta Barkindo Sa'idu, ta ce mutane da yawa da ta ceto sun tagayyara kuma asibitoci da ya kamata a kai su ma ruwa ya malale.
Mutune fiye da miliyan daya da ambaliyar da ta afkawa Maiduguri a ranar talata ta shafa dai sun rasa matsugunnansu kuma akasari basu da ma inda za su kwantar da hakarkari. A yayin da aka koma karatu a makarantun Furamare da Sakandare a Litinin din da ya gabata, ala tilas hukumomi suka garkame makarantun ciki kuwa har da fitacciyar Jami'ar Maiduguri ta Unimaid.
Rahotanni dai na cewa akwai daruruwan mutane wadanda iftili'in ya shafa a yankunan karkara kuma su na ci gaba da tururuwa zuwa babban birnin jihar Maiduguri domin neman mafaka da kuma sauran kayan agaji. Babu shakka alkaluma kan asarar da aka tafka za su ci gaba da fitowa a yayin da mummunar ambaliyar irinta ta farko cikin shekara talatin da birnin maiduguri ya shaida ta fara tsagaitawa.