Zargin tsohuwar ministar Najeriya da cin hanci
August 23, 2023A sanarwar da ta fidda hukumar ta ce ana zargin Diezani Alison-Madueke da karbar cin hanci na tsabar kudi Fam dubu 100 da motocin hawa da tikiten balaguron shakatawa a lokacin da take rike da mukamin ministar mai fetur domin bayar da wasu kwangilolin makamashin Iskar Gas na makuddan kudade.
Karin bayani: Tsohuwar ministar man fetur ta Najeriya na fuskantar tuhuma
Diezani wacce a halin yanzu ke zaune a birnin Landon za ta bayyana a gaban kotu a ranar biyu ga watan Oktoba mai zuwa domin wanke kanta daga wadannan zarge-zarge da ta dade tana musantawa.
Karin bayani: Najeriya: Kotu ta kwace kadarorin Diezani
Dama dai baya ga wannan laifi, ana zargin tsohuwar ministar da laifin halasta kudin haram a Amurka da Birtaniya da kuma Italiya, baya ga tuhuma kan laifin yunkurin karkata sakamakon zaben Najeriya na 2015 da hukumar EFCC ta yi mata.
Karin bayani: Najeriya ta tabbatar da tsare tsohuwar ministar harkokin man fetur din kasar.
Diezani Alison-Madueke mai shekaru 63 da haihuwa ta kasance kusa a gwamnatin Goodluck Jonathan tsakanin shekarun 2010 zuwa 2015, kuma ta rike mukamin shugabancin kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta OPEC.