Nijar: Bita kan zaben da ya gabata
February 23, 2022Sanin kowa ne dai zaben shugaban kasar da ya gudana a Jamhuriyar ta Nijar ya bar baya da kura, inda har yanzu ake jiran sakamakon karar da 'yan adawa suka shigar a gaban kotun ECOWAS ko CEDEAO. Matakin da Hukumar Zaben ta Nijar CENI ta dauka tun yanzu, na da muhimmanci ganin yadda kullum sai wuri ya kure ake tattauna muhimman batutuwa kan harkokin zabukan a Jamhuriyar Nijar. Jinkirin tattauna muhimman batutuwan dai, na haifar da babban rudani da cece-kuce a tsakanin 'yan siyasa da kungiyoyin farar hula masu sa ido kan harkokin zabe. Manyan kungiyoyi na kasa da kasa na taka rawar gani a harkokin shirya zabe a kasashe masu tasowa, a wani mataki na kamawa 'yan kasar shirya zabe mai inganci.
Wannan mataki na Hukumar Raya Kasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ta PUNDD dai, yunkuri ne da ake kira da mai zurfin idanu da wuri yake soma kuka. Zaman bitar ayyukan Hukumar Zaben kasar ta Nijar, an yi shi ne da dukka bangarori da suka hadar da wakilan kungiyoyin farar hula da 'yan siyasa da jami'an tsaro. Kuma a cewar Boukar Sabo mai kula da harkokin zabe a jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki a Nijar din, sun yaba da tsarin sosai. Shi kuwa Kane Kadaure Habibou mai magana da yawun gungun jam'iyyun adawa da suka marawa dan takara na bangaran adawa Alhaji mahamane Ousman baya cewa ya yi, tilas sai an sa masu kishin kasa a gaba idan ana son kaucewa duk wani cikas.