Blinken ya fara sabon rangadi a Gabas ta Tsakiya
February 5, 2024Wannan ne karo na biyar da jami'in diflomasiyyar ke zuwa yankin tun bayan fara rikincin Isra'ila da kungiyar Hamas wanda ke cika watanni biyar da barkewa a wannan makon. Bayan Saudiyya, ziyarar za ta kaishi kasashen Qatar da Masar da Isra'ila da kuma yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan.
Karin bayani: Isra'ila da Hamas na nazarin daftarin tsagaita bude wuta
A daidai lokacin da ya fara wanna rangadin, Firaministan Isra'ila Benjamin Netenyahou ya ce ba zai amince da sharudan da kungiyar Hamas ta gindaya ba kan sakin ragowar mutanen da take garkuwa da su.
A daya gefe kuma ministan harkokin wajen kasar Faransa Stéphane Séjourné wanda shi ma ya kai ziyara Israila ya shaida wa Netenyahou cewa dole Isra'ila ta kawo karshen muzgunawar Yahudawa da ke zaune a yankunan Falasdinawa da suka mamaye a birnin Kudus da bangarorin biyu ke takaddama a kansa.