1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta dau alhakin wasu hare-hare a Najeriya

July 13, 2014

Shugaban kungiyar Abubakar Shekau ya fitar da wani sabon faifayen bidiyo inda ya ce su suka kai hare-hare na kunar bakin wake a wasu manyan biranen Najeriya.

https://p.dw.com/p/1Cc5M
Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau 12. Mai
Hoto: picture alliance/AP Photo

Imam Shekau dai ya fito a sabon faifayen bidiyon da damara ta yaki kewaye da manyan kwamandojinsa, inda ya ce su ne suka kai harin nan a cibiyar kasuwanci ta EMAB Plaza da ke Abuja da tagwayen hare-haren nan na Jos da ke jihar Filato gami da wanda aka kai makarantar koyon aikin duba gari a Kano.

Jagoran na Boko Haram ya kuma sake jaddada cewar kungiyarsu ba za ta saki 'yan matan nan na Chibok da ke hannunsu ba har sai gwamnatin Najeriya ta saki mayakansu da ta ke tsare da su.

Baya ga wannan kuma, Imam Shekau ya jinjina tare da mika wuya ga kungiyar nan ta ISIS musamman ma shugabanta Abubakar Albagdadi dangane da fafutukar da yake ta kafa daular Musulunci.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Mohammad Nasiru Awal