1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo

Al Amin Suleiman Muhammad/AHSeptember 14, 2016

Kungiyar Boko Haram ta fitar da wani sabon bidiyo da ke nuna yadda mayakan kungiyar suka gudanar da Sallah Layya a wuraren daban-daban da suke da iko da su a yankin Arewa maso gabashin Najeriya.

https://p.dw.com/p/1K1zh
Nigeria Terror Leiter der Terrorgruppe Boko Haram Sektenführer Imam Abubakar Shekau
Hoto: AP

Kungiyar Boko Haram ta futar da wannan sabon faifayin bidiyo ta kafar sadarwar ta intanet watau Youtube inda aka nuna yadda mayakan kungiyar suka yi sallah a wasu wurare da ba a bayyana ba. A cewar wanda ya yi limanci a daya daga cikin wuraren wanda kuma ya yi jawabi a faifayin bidiyon wanda ke da tsawon mintuna 13 ya ce an nadeshi ne a ranar Litinin da ta gabata ranar sallah.

Muhawara da jama'a ke yi a game da rashin ganin hoton Abubakar Shekau a bidiyon

Sabon faifayin bidiyon dai bai fayyace komai a kan ikirarin sojoji na raunaya ko ma hallaka shugaban kungiyar Abubakar Shekau a wani hari a cikin watan da ya gabata, inda kawai suka jaddada cewar karkashin jagorancinsa suke har ya zuwa yanzu.Rashin fitowar shugaban kungiyar a wannan faifayin bidiyo kamar yadda ta saba ya haifar da ayar tambaya tsakanin ‘yan Najeriya da ke ganin watakila abin da sojojin Najeriyar ke fada na raunatashi ko hallakashi ya zama gaskiyya.

Nigeria Boko Haram Terrorist
Hoto: picture alliance/AP Photo

Har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta mayar da martani ba

Ya zuwa yanzu dai gwamnati ta Najeriya ba ta ce komai ba kan fitowar wannan sabon faifayin bidyo wanda ake ganin sabon kalubale ne ga gwamnatin da ma rundunar sojojin Najeriya wacce da farko ta yi ikirarin samun nasara a kan kungiyar.

Nigeria Boko Haram Abubakar Shekau Archiv
Hoto: picture alliance/AP Photo