1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Boko Haram ta musunta yarjejeniyar sulhu

Mouhamadou Awal BalarabeOctober 31, 2014

Bayan da gwamnatin Najeriya ta ce ta yi sulhu da Boko Haram, kungiyar ta cigaba da kai hare-hare kafin ta fitar da bidiyon da ke bayyana matsayinta.

https://p.dw.com/p/1DfM1
Nigeria Terror Imam Abubakar Shekau von Boko Haram
Hoto: picture-alliance/AP

Kungiyar Boko Haram ta musanta duk wata tattaunawa domin yin sulhu da gwamnatin Najeriya inda ta yi alwashin ci gaba da yaki da gwamnatocin Najeriya da ma na kasashen Afirka. Jagoran Kungiyar ta Boko Haram wanda aka fi sani da Imam Abubakar Shekau ya fayyace matsayin kungiyar dangane da sanarwar da gwamnmatin ta fitar na yin sulhu da ita.

Wannan dai na kunshe ne a wani sabon sakon faifayin bidiyo na tsawon mintuna sha daya da kungiyar ta fitar wanda aka rabawa manema labarai. Shugaban kungiyar ya kuma jaddada cewa su ba su shiga kowace yarjejeniya da gwamnatin Najeriya ba, haka kuma babu wani da suka wakilta, ya yi magana a madadin ta inda ya ce suna nan suna rike da dalibai matan nan sama da dari biyu.