Boko Haram ta sake tada fitina a Borno
June 22, 2017Talla
Kungiyar Boko Haram ta umurci mazauna wasu kauyuka na jihar Borno da su kwashe nasu ya nasu su bar matsugunansu, abinda ya haifar da fargabar shirin kai hari. Dama ta yi ikirarin sace 'yan sanda mata 16, lamarin da sa gwamnatin tarayyar Najeriya nuna damuwa kan karuwar hare-haren ta'addanci.