Shugaba Buhari na fuskantar barazanar tsigewa
July 28, 2022'Yan majalisun tarrayar Najeriya biyu sun rika biyan bukatar gwamnatin kasar a kusan ko yaushe, lamarin da ya kai ga zarginsu da fadawa aljihun 'yan mulkin kasar. Sai dai danyen ganyen na shirin karewa, inda 'yan majalisun suka bai wa shugaban kasar wa'adin makonni shida na kawo karshen rikicin rashin tsaron kasar ko kuma ya fuskanci barazanar tsigewa. Wannan ne dai karo na farko a shekaru uku da doriya da majalisun ke nuna wa shugaban kasar jan kati bisa rawar da yake takawa a harkar ta tsaro.
Matsayin bangaren 'yan adawa da masu mulki
Duk da cewa jam'iyyun adawa a majalisar dattawa ta kasar ne suka fara wannan yunkuri, amma barazanar tsigewar ta yadu zuwa 'yan jam'iyyar APC ta shugaban kasar. Yusuf Shitu Galambi, dan majalisar wakilai daga jam'iyyar APC mai mulki, ya ce babu alamun gaskiya bisa rawar Buhari ga kokarin warware matsalar ta tsaro.
Daga dukkan alamu, sabuwar barazanar na shirin yamutsa lamura cikin kasar da ke fuskantar jerin rigingimu iri-iri a halin yanzu. Wata sanarwar fadar gwamnatin Najeriya ta kira rawar 'yan dokar da sunan wasan yara.Lai Mohammed, ministan labarai na kasar kuma kakakin gwamnatin kasar ya ce: " Ba batu ba ne da shugaban kasa ke yi wa rikon sakainar kashi, amma dai ba zan iya shaida muku matakan da gwamnati ke dauka a kan batun rashin tsaro ba. Ga masu wannan barazanar tsige shugaban kasa, ina jin ya fi kama da farfaganda, kuma abu ne na dariya."
Me kundin tsrain mulkin Najeriya ya tanada ?
Duk da cewa an sha barazanar tsige shugabannin kasar, amma har ya zuwa yanzu babu tarihin iya kaiwa ga tsige shugaban kasa a tarrayar Najeriya. Kundin tsarin mulkin kasar ya tanadi ratabba hannun kashi biyu a cikin uku na masu doka ta kasar kafin a iya kaiwa ga fara babban aikin tsige shugaban kasar.Faruk BB Faruk da ke sharhi kan siyasa ta kasar ya ce da kamar wuya a tsige shugaban kasa a tarrayar Najeriyar saboda jam'iyyar APC na takama da rinjaye babba a majalisa.
Majalisar tsaron kasar na shirin dorawa a wani taron neman mafitar rikicin da ke nuna alamun wucewa da sanin 'yan mulkin Najeriya.