Buhari ya gana da Merkel ta Jamus a taron G7
June 8, 2015Shugabannin da suka hada da Barack Obama na Amirka da Francois Hollande na Faransa da David Cameron na Birtaniya, sun amsa gaiyata ne daga mai masaukinsu, shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel, inda suka duba batun tattalin arziki da kare muhalli da hanyoyin karfafa tsaro da yaki da aiyukan ta'addanci a duniya. Daga baya a yau Litinin, shugabannin bakwai sun kuma gana da takwarorinsu na wasu kasshe masu tasowa, ciki har da Muhammadu Buhari na Najeriya, kan yadda za a sami hadin kai a fannonin yaki da tarzoma da bunkasar tatalin arziki.
Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel da ke jawabi ga manema labarai a karshen taron kolin, ta kwatanta shi a matsayin taron da ya sami gagarumar nasara, tare da nunar da cewar wadannan kasashe bakwai, ba ma karfinsu na tattalin arziki ko jin dadin rayuwar al'ummarsu ne kadai suka hade su wuri guda ba, amma har suna da wasu manufofi na hadin gwiwa tsakaninsu, wadanda suka hada har da darajar democradiya da kare hakkin dan Adam da kuma kyama ga duk wasu aiyuka na ta'addanci a duniya baki daya.
A lokacin ganawar da aka yi a Schloss Elmau da ke Jihar Bavaria, inji Angela Merkel, shugabannin bakwai sun duba al'amura masu muhimmanci ciki har da kasar Ukraine da batun tattalin arziki da hanyoyin yaki da cutuka a duniya da kuma hanyoyin rage gurbacewar yanayin sararin samaniya.
Shugabannin sun amince da manufofi na hadin gwiwa da za su gabatarwa babban taron mashawartar Majalisar Dinkin Duniya kan batun raya kasa, idan majalisar ta fara taron ta a watan Satumba mai zuwa.
Taron na manyan kasashen yamma bakwai, ko G7 a takaice, ya amince da bukatar kara tashi tsaye domin yaki da yaduwar cutuka, kamar Ebola tsakanin kasashe, inda suka ce tilas ne a dauki matakan kyautata hanyoyin kiwon lafiya a kasashe da dama. Dangane da haka kuwa, ana bukatar hadin kai da tsara manufofi da za su dace da cimma wannan buri.
Taron kolin ya yi nazarin dangantaka tsakanin manyan kasashen bakwai da Rasha, musaman bayan da aka kore ta daga rukunin na manyan kasashe, sakamakon mamaye yankin Kirimiya da gabashin Ukraine.
A game da kasar Girka Merkel ta ce lokaci yana kurewa a game da tattaunawar neman ceto kasar daga rushewar tattalin arziki. Kasashen Turai da hukumar kudi ta duniya, IMF, suna nuna matukar zumunci ga kasarta Girka, amma ana kuma bukatar hadin kai sosai tsakaninsu da wannan kasa yadda za a shawo kan matsalolin.
Taron ya tabo batun cinikayya a duniya baki daya, musaman neman yarjejeniyar da aka santa da suna TTIP tsakanin Amirka da kasashen Turai. Shugaban Faransa, Francois Hollande ya yi marhabin da burin kasashen bakwai na bin manufofin yaki da gurbacewar muhalli. Ranar Litinin shugabannin na manyan kasashen bakwai sun gana da takwarinsu na wasu kasashe masu tasowa, ciki har da shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, wanda ya zo da bukatun kasarsa ga manyan kasashen na duniya. Wadannan bukatu sun hada har da neman taimakon yaki kan kungiyar Boko Haram, wadda ta yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tun daga shekara ta 2009. A karshen tattaunawar da shi, shugabar gamnatin Jamus, Angela Merkel ta ce kasashen za su ba da gudummuwar yaki da kowane irin salo na tarzoma a duniya, daga kungiyar Boko Haram ne ko kuma daga kungiyar IS.