Najeriya za ta mata kaimi ga barayin mai
August 19, 2022Talla
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriyar dai, ya ce gwamnatinsa za ta yi fito-na-fito da masu satar danyen man kasar, mako guda bayan da hukumomin Najeriyar suka cafke wata tankar dakon mai ta barauniyar hanya a gabar tekun Guinea. Shugaban ya ce ko kadan Najeriyar ba za ta amince wasu batagari su dinga amfani da dimbin arzikin danyan man fetur din da kasar ke da shi yadda suka ga dama ba, saboda hakan ya umarci jami'an gwamnatinsa da su kawo karshen wannan matsala musamman ma a yankin Niger Delta da ke Kudu maso Gabashin kasar da kuma ke da arzikin man fetur din. Najeriyar dai na da bukatar hada kai da makwabtanta domin kawo karshen wannan matsalar cikin gaggawa, a cewar wata sanarwa da fadar shugaban kasar ta fitar.