1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Buhari zai yi hutun kwanaki goma a Landan

Mouhamadou Awal Balarabe
August 2, 2018

Shugaba Buhari na Najeriya zai fara hutu a Landan a ranar Jumma'a a daidai lokacin da wasu kusoshin jam'iyyarsa ta APC ke canjin shekar siyasa. Ya saba zuwa wannan birni don duba lafiyarsa.

https://p.dw.com/p/32Vhq
Muhammadu Buhari
Hoto: DW/I. U. Jaalo

Shugaban Najeriya Janar Muhammadu Buhari zai fara hutunsa na shekara-shekara a birnin Landan a ranar Jumma'a, ba tare da an san ko zai yi amfani da wannan dama wajen duba lafiyar jikinsa ba. kakakin fadar shugaban kasa Femi Adesina da ya ba da wannan labarin, ya nunar da cewar mataimakin shugaban kasar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo zai yi rikon kwarya na wadannan kwanaki goma.

Shi dai shugaba Buhari ya saba zuwa Landan babban birnin Birtaniya bisa dalilai na kiwon lafiya. A watan Mayun da ya gabata ma  sai da shugaban Nijeriya ya yi kwana uku a Landan don duba lafiyarsa, baya ga watanni biyar da ya shafe a bara don magance cutar da har yanzu ba a bayyana wa jama'a ba.

Wannan hutun ya zo a daidai lokacin da jam'iyyarsa ta APC da ke mulki ta fada cikin rikici sakamakon canjin sheka na wasu kusohinta suka yi, tare da haifar da kace-nace dangane da lafiyar Buhari mai shekaru 75 bayan da ya bayana aniyar sake tsayawa takara a zaben shekara mai zuwa.