Falasdinu: Isra'ila a Yammacin Kogin Jordan
August 29, 2024Bayan kwashe mako guda da kaddamar da samamenta a yanakin na Gabar Yamma da Kogin Jordan da ya halaka wadanda ta kira jagororin 'yan ta'adda 11, Isra'ila ta nemi mazauna garuruwan Jenin da Tulkarm da su fice daga cikinsu saboda sun zama filin daga. Kakakin sojojin Isra'ilan Daniel Hagary ne ya bayyana hakan, inda ya ce hadarin ta'addancin wadannan gungun miyagun da suke farauta a wannan yankin bai takaita kan Isra'ila da suke alwashin share ta daga doron kasa ba har ma da su kansu sauran Falasdinawa masu kaunar zaman lafiya da Tel Aviv din. A yayin da rundunar sojojin ke nuni da cewa ficewar mazauna yankunan kimanin su 6000 na wucin gadi ne daga baya zasu dawo, masu tsattsauran ra'ayin a Isra'ilan cikinsu har da ministan harkokin wajenta Israel Katz na kira da a mayar da yankin na Gabar Yamma da Kogin Jordan tamkar yankin Gaza. Tuni dai Majalisar Dinkin Duniya a sakon da sakatarenta Antonio Guterres ya wallafa a shafinsa na X, ya yi kira ga Isra'ila ta gaggauta dakatar da ayyukan sojojinta a Gabar Yamma da Kogin Jordan din da ta mamaye. Ya ayyana matakan nata da na tsokana da neman tashin hankalin da ba za a lamunta ba, tare kuma da siffanta yunkurin korar Falasdinawa daga yankin da aikin da ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Tun kusan watanni shidan da suka gabata ne dai, 'yan share wuri zauna da ake zargin ministan cikin gidan Isra'ila Itamar Ben-Gvir na kara zugawa, suka fara kaddamar da farmaki kan Falasdinawa mazauna yankunan Gabar Yamma da Kogin Jordan da kone musu gidaje da dukiyoyinsu. Ana dai tunanin sun kai wannan farmakin ne da nufin tirsasa musu fita daga yankin baki daya domin ya zama mallakarsu su kadai, lamarin da ya janyo kakkausar suka daga Amurka da kasashen Yamma da ma kungiyoyin kare hakin dan Adam. A nata bangaren, Hukumar Falasdinawa ta yi kira ga kasashen duniya da su dauki duk matakan da suka wajaba na hana ci gaban abun da ta kira kisan kare dangin da Isra'ila ta dauko shi daga Zirin Gaza take neman sai ta dangana da yankin Gabar Yamma da Kogin Jordan din. A yayin da kungiyar Hamas ta bayyana cewa, irin ayyukan ta'annutin da Isra'ilan ke yi wa Falasdinawa a ko ina, wata manuniya ce da ke tabbatar da gaskiyar zabin da ta dauka tun da fari na 'yanta al'ummar Falasdinawa ta hanyar gwagwarmaya kadai ba ta hanyar lallama da tattaunawa da Isra'ila kamar yadda gwamnatin Mahmud Abbas da ke mulkin a yankin na Gabar Yamma da Kogin Jordan din ke dauka.