1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bukatar taimakon jin kai a Najeriya da tafkin Chadi

January 24, 2017

Dubban daruruwan mutanen da rikicin Boko Haram ya tagaiyara a Najeriya da kuma kasashen yankin tafkin Chadi suna cikin matsanancin hali na bukatar taimakon jin kai na gaggawa.

https://p.dw.com/p/2WKvz
Nigeria Flüchtlinge wegen der Offensive gegen Boko Haram
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Jami'in tsare tsaren ayyukan taimakon jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a yankin Sahel Toby Lanzer yace akwai mutane miliyan goma sha daya wadanda ke tsananin bukatar taimakon jin kai a Najeriya da yankin tafkin Chadi.

Jami'in na Majalisar Dinkin Duniya ya shaidawa manema labarai cewa mutane fiye da miliyan bakwai wadanda ke fama da matsanancin karancin abinci da kuma ke zaune cikin halin rai kwakwai mutu kwakwai da kyar suke samun abinci sau daya a rana.

Tarzomar Boko Haram da kuma fafatawar da sojoji ke yi da su ya raba mutane fiye da miliyan biyu da muhallansu. Kungiyoyin agaji wadanda suka sami shiga yankunan da sojojin suka 'yanto daga yan Boko Haram sun ce halin da kungiyar ta jefa al'ummar yankin abin damuwa ne matuka.