Bukola Saraki ya noke wa kotu a Abuja
September 21, 2015Sannu a hankali dai batu na shari'a na neman rikidewa ya zuwa na siyasa a tarrayar Najeriya, inda da ranar Litinin din nan kotun da ke shari'ar kaddarori na jami'an gwamnati ta share tsawon wuni a cikin shari'ar shugaban majalisar amma kuma ba tare da ganin keyarsa cikin zauren kotun ba.
To sai dai kuma harabar kotun ta koma dandali na magoya baya da suka cika harabar kotun suna wake waken goyan baya a gareshi da tsinuwa ga daya a cikin jiga jigan jam'iyyar Bola Ahmed Tinubu.
Tuni dai Sarakin da kotun ta zarga da karya wajen bayanan kadarorinsa a shekaru 12 da suka gabata ya kira siyasa da kokari na ganin bayansa a bangaren wasu 'ya'yan jam'iyyar tasa ta APC.
Magoya bayan na Bukola Saraki dai na ambato Bola Ahmed Tinubu da kuma Nasiru Ahmed El Rufa'i da ke zaman gwamnan jihar Kaduna a yanzu a matsayin masu tunanin Sarakin ba shi da sarari a cikin jirgin APC da ke sararin samaniyar Allahu a yanzu.
Abun kuma da a cewar Tukur Ibrahim El Sudi da ke zaman mashawarcin na Saraki kan harkar shari'a ya sa su bakin rai bakin fama da nufin tabbatar da kare 'yancin nasa da ma mummunar guguwar siyasar da ke dada turnuku a yanzu.
Akalla 'yan majalisar dattawan kasar 55 ne da mafi yawansu ke zaman 'ya'yan jam'iyyar PDP ta adawa ne suka gana suka kuma ce suna da yakini na kare shugaban nasu da suke zargin fadar gwamnatin kasar da hannu a kokari na rushe masarautar ta Saraki.
To sai dai kuma wata sanarwar fadar gwamnatin kasar dai ta ce babu hannu a cikin rikicin na Saraki, kuma shugaba Buhari ba shi da niyar tsoma baki da nufin hana doka kan aikinta.
A tunanin Bello Sabo Abdulkadir da ke zaman manazarcin harkoki na siyasar kasar, gwagwarmayar cikin APC na iya kaiwa ga illa babba ga makomar jam'iyyar anan gaba.