1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Burkina Faso ta dakatar da shirye-shiryen BBC da VOA

April 26, 2024

Burkina Faso ta dakatar da shirye-shiryen kafafen yada labarai na BBC Africa da Muryar Amurka VOA har na tsawon makonni biyu sakamakon yada labarin da Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Human Rights Watch ta bayar.

https://p.dw.com/p/4fEIU
Burkina Faso, Ouagadoudou | Ibrahim Traore
Hoto: Kilaye Bationo/AP/picture alliance

Labarin na HRW ya zargi sojojin kasar ne da kisan mutane babu gaira babu dalili kamar yadda hukumomi suka bayyana a daren Juma'a.

Rahoton binciken na kungiyar ya ce sojojin kasar ta yammacin Afirka sun kashe wasu mutanen karkara akalla 223 ciki har da kananan yara 56 a watan Fabrairu.

 

Karin bayani:Harin ta'addanci a masallaci da coci a kasar Burkina Faso ya halaka mutane da dama

 

Kisan mutanen wani yunkuri ne na kakkabe fararaen hula da aka zarga da hada kai da masu tada kayar baya a cewar rahoton.

 

Ana zargin sojojin Burkina Faso da kashe fararen hula 223

 

Hukumomin kasar ta Burkina Faso a cikin wata sanarwa sun umurci kamfanonin sadarwar intanet su katse hanyoyin sadarwa ga shafukan intanet na BBC da kuma VOA da ma ita kanta kungiyar HRW.