Burkina Faso ta rufe shafin DW kan kwarmata kisan kiyashi
April 29, 2024Dama kungiyar Human Rights Watch ta yi zargin sojoji da halaka mutane sakamakon taimaka wa masu ikrarin jihadi da ke dauke da makamai.
Karin bayani: Burkina Faso ta yi fatali da zarge-zargen Human Rights Watch
Sai dai hukumomin kasashen Amurka da Burtaniya sun nuna damuwa dangane da kisan na fararen hula da ake zargin sojojin kasar da aikatawa, a wata sanarwar hadin gwiwa da gwamnatocin kasashen biyu suka fitar.
Karin bayani: Ana zargin sojojin Burkina Faso da kashe fararen hula 223
Hukumomin Burkina Faso sun dakatar da ayyukan kafafen yada labaran kasashen ketare a kasar ciki har da shafin Internet na Deutsche Welle na kasar Jamus da jaridun Faransa da suka hadar da Le Monde da Ouest-France, har ma da jaridar The Guardian ta kasar Burtaniya da kuma wasu kamfanin dillancin labarai na Afirka.