Burtaniya ta kafe kkan kudurinta na tura bakin haure Rwanda
March 21, 2024Gwamnatin Burtaniya ta ce har yanzu tana kan bakanta na kokarin aikewa da 'yan gudun hijirar cikin kasar zuwa kasar Rwanda nan da watanni masu zuwa, duk kuwa da takaddamar da ta kaure a zaman majalisar wakilan kasar a Alhamis din nan.
Karin bayani:Rishi Sunak: Ruwanda tudun mun tsira ce
Kudurin dai na zama wani mataki da firaminista Rishi Sunak ya dauka don dakile kwararar masu neman mafaka a Burtaniya, tare da takaita asarar rayukan 'yan ci-ranin da yunkurin tsallakawa zuwa Turai a cikin ruwa.
Karin bayani:Birtaniya za ta kori baki zuwa Ruwanda
Mr Sunak ya gabatar da sabon kudurin da aka yi wa kwaskwarima ne a karshen shekarar da ta gabata, bayan da kotun kolin Burtaniya ta haramta kai masu neman mafakar zuwa kigali, kasancewar hakan ya saba da dokar kasa da kasa.