1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Burundi ta kulle iyakarta da Ruwanda

January 11, 2024

Kasar Burundi ta ce ta rufe iyakarta da Ruwanda sakamakon zargin da take yi wa makwabciyarta na taimaka wa 'yan tawaye wajen kai farmaki a yankunanta.

https://p.dw.com/p/4b98L
Iyakar kasar Burundi da Ruwanda
Iyakar kasar Burundi da RuwandaHoto: Stephanie Aglietti/AFP/Getty Images

Burundi ta ce kungiyar RED-Tabara ta kai wani hari a ranar 22 ga watan Disambar shekarar 2023 wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane kimanin 20 ciki har da yara da kuma mata a kusa da iyakarta da  Jamhuriyar Dimukuradiyar Kwango.

Shugaba Evariste Ndayishimiye na Burundi ya zargi Ruwanda da taimaka wa 'yan tawayen kai wannan hari, zargin da Ruwanda ta musanta. A cikin sanarwar da ma'aikatar cikin gida ta Burundi ta fitar, ta ce ta yanke dukannin wata alaka da Shugaba Paul Kagame.

Dama dai dangantaka ta sha yin tsami tsakanin kasashen biyu. Tun a shekarar 2015 ne kungiyar RED-Tabara dai ta sha kai hare-hare a kasar da ke gabashin Afirka, sai dai kuma an daina jin duriyarta tun daga watan Satumbar 2021 bayan ta kai wasu jerin hare-hare ciki har da na filin jirgin saman birni Bujumbura.